Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin watsa labarai na Ibrananci sun ruwaito: “Amfani da jiragen sama marasa matuki na Fiber-optic da Hizbullah ke yi a yaƙin ya haifar da sabon ƙalubale ga rundunar Isra'ila”.
Bisa lura da cewa dabarun yakin Hizbullah ta yi anfani da a kudancin Lebanon sun bayyana wani sabon ƙalubale ga rundunar Isra'ila, kafofin watsa labarai sun rubuta: A lokacin ayyukan ƙasa a Lebanon, jami'an Hizbullah sun yi amfani da ɗaruruwan jiragen sama marasa matuki da ke ɗauke da abubuwan fashewa waɗanda su ke aiki ta hanyar amfani da fiber-optics, ba ta hanyar sadarwa ta waya ko ta tauraron ɗan adam ba. Sakamakon haka, rundunar Isra'ila tana fuskantar matsala wajen kame waɗannan jiragen, wanda ya haifar da asarar rayuka da yawa a tsakanin rundunoninta.
Kafofin watsa labarai na Ibrananci sun ƙara da cewa: Da farko, rundunar sojin ta yi imanin cewa za a iyakance yawatawar wadannan jiragen sama marasa matuki na waɗannan jiragen zuwa kilomita biyu. Duk da haka, a lokacin yaƙin, ya bayyana cewa zangonsu ya wuce kilomita 10.
A cewar waɗannan rahotannin kafofin watsa labarai, rundunar sojojin da ke mamaya ta fahimci cewa jiragen sama marasa matuƙa na fiber optic ƙalubale ne da ke buƙatar sojojin Isra'ila da masana'antar tsaron Isra'ila su nemo hanyoyin fasaha don magance su da kuma shawo kansu.
Your Comment